1. Home /
  2. Other /
  3. Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai.


Category

General Information

Phone: +1 902-244-0254



Likes: 4350

Reviews

Add review



Facebook Blog

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 11.05.2021

Manhajar "Html Viewer and Editor" manhajace wadda ake rubuta tsarin rubutu na HTML wadda yake nufin HYPER TEXT TRANSMISSION MARK-UP LANGUAGE. HTML tsarine na rubutu da yake zayyanawa na'urar komfiwta ko waya yadda zai bayyana shafin yanar gizo ko na manhaja a wani lokacin. Alal misali. Yayinda kake son zayyanawa na'urar komfiwta ko waya akan ya bayyana rubutu da layi a kasansa to sai ka rubuta:... Rubutu mai layi. To kaga idan na'urar ya tashi bayyana shafin sai ya sanya layi a kasan inda aka rubuta "Rubutu mai layi." To kuwa da taimakon wannan manhaja na Html viewer and editor ne ake wadannan dabarun. Zaka iya samun wannan manhaja a dandalin Google play store domin saukewa a wayarka.

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 06.05.2021

Manhajar Microsoft Paint wadda aka fi sani da 'Paint' ko 'Ms Paint' manhajace wadda ake samunta a na'urar komfiwta domin yin zane-zane da kuma kawata zanen. Haka zalikama ana iya sauke wannan manhajar a wayoyin android da makamantarsu. Wannan zanen da yake kasa zane ne wadda akayi da manhajar Paint na wayar android. Domin sauke naka kaima zaka iya ziyartar dandalin yanar gizo na Google play store domin saukewa. Mun gode.

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 23.04.2021

Ga yadda zaka duba QR CODE a whatsapp.

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 07.04.2021

Kafar sada zumunta ta Whatsapp wata manhajace wadda ake iya sadarwa tsakanin na'urorin waya ko komfiwta. A sabdo hakane kafar ya zamanto mai matukar amfani ga mutane, musammanma a duniyarmu to yau. Iyaye suna da matukar hakki akan yaransu , yana da kyau ace iyaye suna bibiyar yaransu a kafofin sada zumunta irinsu facebook da whatsapp d.s domin su rinka ganin irin abokan da yaransu suke mu'amala da su. Kama daga hirarrakinsu da kuma musanyar sakonninsu d.s. Manhajar WHA...TSCAN na daya daga cikin irin manhajojinda ake iya bibiyar mutum ta whatsapp. Domin yin hakan gabatar da wadannan hanyoyi kamar haka: A. Jeka Google play store sannan ka sauke manhajar "Whatscan" B. Ka bude shi sannan kayi scanning (tantance) din wani abu da ake kira QR CODE na whatsapp din da yake wayar yaron naka. See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 19.03.2021

HANYAR DA ZAKA BI DOMIN GANE ABUBUWAN DA AKAYI DA WAYARKA. Domin ganin wuraren da wani ya shiga da wayar ka to sai ka bi wadannan matakai: A..Sai ka saka * # *# 4 6 3 6 # * # * sannan ka aika. B..Zai bayyana maka wani shafi sai ka zabi "Testing" C..Zabi "Usage statistics"... D..Zai bayyanar maka da wani shafi da ke dauke da jerin guraren da aka shiga da wayar dama lokuta. See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 08.03.2021

YADDA ZAKA KARAWA BATIRIN WAYARKA KARFI. 1. Sai kaje dandalin yanar gizo na google play store sannan ka saukar da wata manhaja mai suna 'phone master' domin wannan manhajar na taimakawa a wajen share duk wani kananan abubuwa da suka zauna a ma'adanin wayar ka, domin kuwa su wadancen abubawan suna samuwane yayin da ka bude wasu manhajojin na musamman tamkar dai kace tarihine na gurbin ajiya na wasu manhajojin. Kuma su irin wadancen abubuwa sune suke sanyawa waya zafi da rash...in sauri da kuma nauyin aiki. 2..Sannan ya zama ka saba share manhajoji marasa amfani a wajenka. 3..Kullum ya zama kana rage hasken wayarka zuwa kasa sosai ko kuma ka sanya shi a yanayin 'yi da kanka' wato 'Automatic'. 4..Ya kasance a koda yaushe sashen sanarwarka a kashe (Notifications) saboda barin sa a kunne yana shan chaji. 5..Ka rinka sanya wayarka a yanayin burgawa (vibration). 6..Ka rinka kashe sashen WiFi naka domin yana nemo adreshin WiFi din da kansa. 7..Kunna yanayin jirgi wato 'Airplane mode' a lokacin da ka san kana wani abu na daban a wayar kamar su kallo ko rubutu d.s amma sai idan matukar baka tsammanin kira. 8..Kashe yanayin 'apps update automatically' wato sabanta manhaja da kansa. 9..Ka rinka kashe 'Location' ko 'GPS' na wayarka a koda yaushe. Wato tsarin gano inda kake a duniya ta waya. Kashe wannan tsari na rage zukar chajin batirin wayarka. 10. Kashe 'Data' na wayarka. Wato tsarin yanar gizo na wayarka. 11. Kashe tsarin Hotspot'. 12. Kashe tsarin 'Bluetooth' 13. Dakatar da manhajojin da suke aiki a bayan fage kamar su; 'Music player', 'Sound recorder'. d.s See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 26.02.2021

WASU MADANNAI TARE DA AMFANINSU. 1. ESC : Ana amfani da shi a wajen dakatar da aiki a na'urar komfiwta. 2. F1: Amfaninsa shine zai bayyana maka allon taimako ko fadakarwa. Wato allone da yake dauke da rubutu game da yadda zaka aiwatarda abubuwa daban-daban. 3. F2: Idan aka taba wannan madannin akan sunan wani fail, to zai bada damar sake masa suna. 4. SHIFT + F7 : Idan aka matsa wadannan madannan a tare, to kuwa zai bada damar duba kuskure a jimlarka.... 5. Caps Lock: Yana kulle nau'in rubutu a manyan harrufa ko kananan harrufa. See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 21.02.2021

Wasu halayya dake tareda na'urar komfiwta. ---------------------------------- . Sauri (speed): na'urar komfiwta ya kan sarrafa miliyoyin sakonni acikin dakiku kadan. . Tabbaci(accuracy): na'urar komfiwta ya kan tabbatar da sarrafa sakonni dai-dai ba tare da kura-kurai ba. . Ajiya (Storage): na'urar komfiwta takan ajiye duk wani sako da ta sarrafa na tsawon lokaci ko kuwa na kankanin lokaci.... . Daki-daki (Versatility): na'urar ta kan sarrafa sakonnine daga mai sauki zuwa mai wahala. .Automation: na'urar komfiwta ta kan yi aikine da kanta matukar aka bukaci tayi hakan. Ma'ana ana bata umarnine sannan tayi aikin ba tare da ka Sanya karfin ka wajen aikin ba. Allon masayi (keyboard). Allon maayi: na'uarane da yake taimakawa komfiwta a wajen shigar da sako domin sarrafawa. Ana amfani da shine a wajen shigar da rubutu (text), umarni (commands) da dai sauransu. Tsayayyen allon masayin na'urar komfiwta da ake kira "desktop" wato komfiwta da fannoninta yake daban-daban. Allon masayin irin wannan komfiwtar tana da madannani dari da daya (101). Ire-iren madannani. A. Madannani masu amfani na musamman (function keys): wadannan wasu madannaine da akayi su domin idan aka dannasu wani aiki na musamman zai faru a cikin na'urar komfiwtar. Sune F1 har zuwa F12. B. Madannai masu dauke da lambobi (numerical keys): wannan kuwa madannanine da suke dauke da lambobi wanda idan aka dannasu sai a ga lamba ta bayyana a allon manuni (monitor). Sune daga 0 zuwa 9. C. Madannai masu aiki tilo (alternative keys): irin wadannan madannan kowane madanni aikinsa dayane kawai, ma'ana kowane madanni an sanya masa aikinsa na musamman kuma daya tak. Sune Alt, Shift, Num Lock da sauransu. D. Madannai masu alamar kibiya (arrow keys): madannaine da ake amfani da su a wajen motsawa zuwa bangarori daban-daban. E. Madanni mai aiwatarwa (control key): shi madannine da ake dannashi a tare da wani madannin domin aiwatarda wani aiki na musamman. Misali akan latsa madannin 'Ctrl da B' a tare domin sanya rubutu su yi kauri. F. Madannai na musamman (special keys): sune irinsu ENTER, HOME, END, PGUP, PGDN, DEL, INS, BACKSPACE, ESC, SPACE, CTRL, ALT da kuma SHIFT. Su yanayin aikinsu na musamman ne domin kuwa suma kowane madanni daya yana aiwatarda wani aiki na musamman. Misali kamar PGUP yana nufin PAGE UP ne a turance wato "SHAFIN SAMA" ma'ana zai kaika zuwa cen shafin sama yayinda kake cikin shafin Microsoft office word.

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 14.02.2021

Na'urar komfiwta. Komfiwta: na'urace wadda take karkashin kulawar wasu tsare-tsare da ake kira "program" , wannan na'urar takan karbi sakonni (data), sannan ta sarrafa shi ya dawo sako mai cikakkiyar ma'ana da ake kira "information". Program. Program: wasu tsare-tsarene da na'urar komfiwta take amfani da su domin aiwatarda ayyukanta.... Hardware. Hardware (abubuwan zahiri). Wadannan wasu fannonine na na'urar komfiwta da ake iya tabawa, gani da kuma jinsu. Hardware sun kasu kashi biyu (2): - Sashen masarrafa (system unit): wannan ya kunshi wasu kananan na'urori dake taimakawa masarrafar wajen aiki, kamar Su; Tsakar masarrafar bayanai (CPU), ma'adani (memory) da sauransu. - Na biyu kuma sune kananan na'urorin da ake makalawa ko sanyawa na'urar komfiwtar daga waje. Misali irinsu na'urori masu shigarwa (input devices) da na'urori masu fitarwa (output devices) da kuma na'urori masu taimakwa wajen sadarwa (communication devices) kamarsu na'urar modem.

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 08.02.2021

Ga masu shafin facebook ga wani riga-kafi. ----- Saboda kaucewa yiwuwar yi maka kutse daga masu kutsen ya kamata a ce ku rinka duba abokanku na facebook lokaci bayan lokaci. Ina nufin ku duba jerin 'FRIENDS' naku idan kuka ga wanda baku sani ba to ku yi kokarin cireshi a jerin abokannaku domin zai iya yiwuwa an yi masa kutsene aka kwace masa shafin nasa. ... Bin wannan hanyar tamkar ace mutum ne ya kamu da wata cuta, to kunga idan aka barshi a cikin sauran zai iya shafa masa, sai dai a cireshi daga masu lafiya. See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 25.01.2021

2_GIRMANSU. Komfiwta ana kasa su bisa ga yadda girmansu yake. Ga ire-iren komfiwta bisa ga girmansu: 1. "Mainframe computer" Shi wannan nau'in komfiwtane da yake da matukar girma sosai. ... Ga alamominsa kamar haka: *Suna da matukar girma tamkar daki. *Suna da dan sauri a wajen aiwatar aiki. *Ba a iya daukarsa daga wani waje zuwa wani wajen. *Suna yin zafi. 2_"Super computer" Shima wannan nau'in yana da girma. Girmansa kamar akwati ko kwali. Suna da sauri sosai sannan suna aiki mai dan yawa Suna da sauri sosai sannan suna aiki mai dan yawa. 3_"Mini computer" Wannan kuwa sune komfiwtocin da basu da girma, matsakaitane a wajen girma. Sune laptop da deskt Wannan kuwa sune komfiwtocin da basu da girma, matsakaitane a wajen girma. Sune laptop da desktop. 4_"Micro computer" Wadannan kuwa komfiwtocine kanana sosai. Kamar wayar salalu, over-over, d.s Suna da karfin masarrafa da kuma ma'adi (memory Suna da karfin masarrafa da kuma ma'adi (memory). See more

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 23.01.2021

An kasa na'urar komfiwta bisa abubuwa guda 3 : 1_ Amfaninsu. 2_Girmansu. 3_Manufarsu.... 1. Amfaninsu. Wannan sun hada da yadda ake amfani da na'urorin ta hanya daban-daban. Sune kamar haka: . 'Hybrid computer' komfiwta mai nuna lambobi da kuma alama. Misali kamar wayar salula, komfiwtar hannu (laptop) d.s . 'Analog computer' komfiwta mai nuna alama. Misali kamar fitalar kan hanya, male. 'Analog computer' komfiwta mai nuna alama. Misali kamar fitalar kan hanya, maleji d.s . 'Digital computer' komfiwta mai nuna lambobi kawai. Misali kamar na'urar lissafi (calculator), na'urar lissafin adadin mai na gidan mai . 'Digital computer' komfiwta mai nuna lambobi kawai. Misali kamar na'urar lissafi (calculator), na'urar lissafin adadin mai na gidan mai d.s

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 15.01.2021

Na'urorin lantarki kamarsu komfiwta, wayar salula d.s a wannan zamani suna taka muhimmiyar rawa a wajen sada karamin zumunci saboda zaka iya ji ko ganin dan uwanka ta yanar gizo, yayinda na'urorin karfe kamarsu mota, mashin, jirgi d.s kuwa suke taimakawa a wajen sada babban zumunci domin zai taimaka maka a wajen tafiye-tafiye domin ziyartar yan Na'urorin lantarki kamarsu komfiwta, wayar salula d.s a wannan zamani suna taka muhimmiyar rawa a wajen sada karamin zumunci saboda zaka iya ji ko ganin dan uwanka ta yanar gizo, yayinda na'urorin karfe kamarsu mota, mashin, jirgi d.s kuwa suke taimakawa a wajen

Koyi ILmin Na'urar Computer da Hausa. Mbamai. 30.12.2020

Manhajar da ake kira Microsoft Office wata manhajace wadda ake amfani da ita a wajen rubutu, tsara rubutun, tsara wasikar Email, tsara shafin yanar gizo, tsara allon rubutu masu motsiManhajar da ake kira Microsoft Office wata manhajace wadda ake amfani da ita a wajen rubutu, tsara rubutun, tsara wasikar Email, tsara shafin yanar gizo, tsara allon rubutu masu motsi d.s A cikin wannan manhajar akwai wasu kananan manhajojin wadanda ake wadancen ayyukan da su. Misali. Akwai kara...mar manhajar Microsot Office Word amfaninta kuwa shine rubutu da tsara rubutun zuwa nau'ika daban-daban. Wannan ya shafi maida rubutu su dan kwanta ko kuma sanya layi a kasan rubutun ko suyi kauri kada A cikin wannan manhajar akwai wasu kananan manhajojin wadanda ake wadancen ayyukan da su. Misali. Akwai karamar manhajar Microsot Office Word amfaninta kuwa shine rubutu da tsara rubutun zuwa nau'ika daban-daban. Wannan ya shafi maida rubutu su dan kwanta ko kuma sanya layi a kasan rubutun ko suyi kauri kadan d.s Hanyoyi biyune ake amfani da su a wajen tsara rubutun sune; 1_hanya ta farko shine hanyar da ake bi ta hanyar amfani da wasu tsare-tsare da yake zuwa a cen saman fuskar manhajar1_hanya ta farko shine hanyar da ake bi ta hanyar amfani da wasu tsare-tsare da yake zuwa a cen saman fuskar manhajar. 2_ Hanya ta biyu kuwa shine ta hanya mai sauki (wato short2_ Hanya ta biyu kuwa shine ta hanya mai sauki (wato shortcut). See more